7 Yuli 2020 - 13:06
Kifewar Kwale-Kwale: Buhari Ya Bukaci A Karfafa Ayyukan Ceto

Shugaban Najeriya, Muhammadu, Buhari ya bukaci a karfafa ayyukan ceto, biyo bayan kifewar kwale-kwale biyu da aka samu a kasar a baya baya nan, wadanda kuma sukayi sanadin rasa rayukan mutane da dama.

(ABNA24.com)  Wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ya fitar, ta kuma isar da ta’aziya ga iyalai da makusantan wadanda suka rasa rayukansu a hadarurukan kwale kwalen guda biyu.

A ranar Lahadi, data gabata gwamman mutane ne suka rasa rayukansu a kifewar wani kwale kwake a kogin jihar Benue dake tsakiyar kasar.

Kafin hakan dama a ranar Juma’a data gabata mutum bakwai sun gami da ajalinsu a lamari irin wannan a garin Ikorodu dake kusa da jihar Lagos.

342/